Inside Arewa Hausa

Labarun Hausa

Labarai Siyasa

Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Aika Da Sabbin Sunayen Ministoci Da Majalisar Dattawa Za Ta Tantance Su

A yau ne shugaban kasa Bola Tinubu zai aika da sabbin sunayen ministoci da majalisar dattawa za ta tantance su.

A cewar wata majiya mai tushe a majalisar dattawa, sunayen zasu zo jiya da daddare ko kuma da sanyin safiyar yau.

Majiyar ta shaida wa wakilinmu cewa za a karanta sunayen sabbin rukunin ministocin da za a tantance a zauren majalisar a yau laraba

Yau ne za a sa ran kammala tantance mutane 28 da aka mika sunayen su domin tantance su yayin da sauran kashin na biyu za a tantance nan gaba.

A ranar Litinin ne Majalisar Dattawa ta tantance 14 daga cikin 28 na Ministoci da Shugaban Kasa ya mika a baya yayin da aka tantance karin mutum 9 a jiya Talata.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *