Inside Arewa Hausa

Labarun Hausa

Labarai

Ambaliyar Ruwa Ta Rusa Gidaje 100, Mutane 500 Sun Rasa Matsugunni A Gombe

Ambaliyar ruwa a garin Dogon Ruwa da ke Karamar Hukumar Kaltungo ta Jihar Gombe ta rusa gidaje 100 yayin da akalla mutane 500 suka rasa matsugunni.

Ruwan saman da aka tafka kamar da bakin kwarya a ranar Alhamis tun misalin karfe 11 na safe zuwa karfe 3 na rana ne ya haddasa wannan gagarumar barna.

Mutanen garin na Dogon Ruwa sun yi ta fama wajen tsamo dukiyarsu da ruwa ya tafi da ita, sai dai lamarin ya ci tura har ta kai ga asarar dabbobi.

Wani shugaban al’umma a garin mai suna Aliyu Isah, Sa’in Dogon Ruwa, ya bayyana cewa ambaliyar ta ba su tsoro inda suka ga gidaje suna ta rushewa kuma jama’a na ta kokarin tsira da rayukansu. Sa’in Dogon Ruwa ya kara da cewa, rijiyoyin da ke cikin gidajen jama’a sun cika makil, wanda hakan ya sa suka kara jin tsoron ko da ambaliyar ta za ta wuce abin da suka yi tsammani.

A cewarsa, yanzu haka dai galibin wadanda almabaliyar ruwan ta shafa aun nemi mafaka ne a harabar wasu makarantu da ke garin.

Dama dai masu hasashen yanayi sun ba da sanarwar cewa a bana za a fuskanci tsawa da ambaliyar ruwa a sassa daban-daban na kasar.

Aminiya ta tuntubi jami’an Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA) Muhammad Garba wanda ya ce sun samu labarin aukuwar ambaliyar amma ba su je garin ba tukuna sai ranar Litinin. Muhammad Garba ya ce zuwa yanzu ba su iya kididdige girman asarar ba tun da ba su kai ga zuwa garin ba sai zuwa gobe Litinin, inda za su gana da jami’an Karamar Hukumar Kaltungo su gudanar da aikin tare sannan su dauki matakin da ya dace.

Jaridar Aminiya

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *