Inside Arewa Hausa

Labarun Hausa

Labarai Siyasa

Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi Sun Shirya Zikiri a Fadar Aminu Ado Bayero-Shugaban Kasa Tinubu Babban Bako

Yuli 05 2024

Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi tana farin cikin gayyatar ƴan uwa Musulmai zuwa taron zikirin Juma’a na shekara a jihar Kano Za a gudanar da taron ne a gobe Juma’a 5 ga watan Yulin 2024 a fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da ke fadar Nassarawa Wannan na kunshe ne a cikin sanarwa da Sayyadi Ibrahim Dahiru Bauchi ya fitar inda ya ce za a yi taron da misalin karfe 4.00 na yamma

Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarautar Kano, Sheikh Dahiru Bauchi zai gudanar da zakiri a fadar Nassarawa.

Gidauniyar Shehin malamin za ta gudanar da taronta na zikirin Juma’a na shekara a fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

Za a yi zikiri a fadar Nassarawa Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sayyadi Ibrahim Dahiru Bauchi ya sanyawa hannu da Masarautar Kano ta wallafa a shafin Facebook.

Za a gudanar da zikirin ne kamar yadda aka tabbatar a Yau Juma’a 5 ga Yulin 2024 a fadar da misalin karfe 4.00 na yamma.

Sheikh Dahiru Bauchi shi ne zai kasance babban baƙo na musamman a wurin taron wanda kuma shi ne ya shirya zikirin.

Ana sa ran manyan bakin da za su halarci zikirin sun hada da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da Shugaba Bola Tinubu. Har Ila yau, a yayin taron za a gudanar da addu’o’i na musamman domin shawo kan matsalolin da ƙasar ke fuskanta a bangarori da dama.

A wani labarin mai kama da wannan, mun kawo muku cewa iyalan Sheikh Dahiru Bauchi sun ziyarci Muhammadu Sanusi II a fadarsa. Tawagar ta kai ziyarar karkashin jagorancin ɗansa mai suna Aminu Dahiru Bauchi domin yin mubaya’a da nuna goyon baya.

Hakan ya biyo bayan ci gaba da dambarwa da ake yi kan sarautar Kano tsakanin Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *