Inside Arewa Hausa

Labarun Hausa

Labarai Matsalar Tsaro

Gwamna Uba Sani Ya Bada Umarnin Bincike Kan Dalilan Da Suka Janyo Asarar Rayukan Mutane 50

Gwamna jihar Kaduna Uba Sani, ya bada umarnin gudanar da bincike kan dalilin da suka janyo asarar rayukan mutane 50 ranar lahadin data gabata a Tudun Biri biyo bayan wani hari da sojojin saman kasar nan suka kai yankin.

Mazauna yankin da abin ya shafa na gudanar da taron Maulidi ne, kwatsam sai sojojin sama suka kai hari bom bisa kuskure lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama yayin wasu suka jikka.

A cikin wata sanarwa da gwamnan ya fitar ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu tare da jajantawa wadanda suka jikka yayin wannan hari.

Uba Sani yace gwamnatinsa zata yi dukkanin wata mai iyuwa domin kaucewa faruwan hakan nan gaba.

Gwamnan ya kara bada tabbacin cewa gwamnatinsa zata cigaba da kara tsare al’ummar jihar da kuma kokarin ganin an kawar da dukkanin ayyukan ‘yan ta’adda. Kazalika Uba Sani, yace yana tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan harkar tsaro domin kaucewa afkuwar irin wannan lamari nan gaba.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *