Inside Arewa Hausa

Labarun Hausa

Labarai Yaki Da Cin Hanci

Kotu Ta Tura Wani Matashi Zuwa Gidan Kurkuku Na Tsawon Watanni 4 Bisa Samunsa Da Laifin Satar Doya

Wata kotu dake zamanta a Dei-Dei dake Abuja, ta tura wani matashi mai suna Felix Adams zuwa gidan kurkuku har tsawon watanni hudu bisa samunsa da laifin satar doya.

Matashin mai shekaru 22 da ba a bayyana addireshinsa ba, ana tuhumarsa da laifin shiga da kuma aikata laifin sata.

Dan sanda mai gabatar da kara Chinedu Ogada, ya bayyanawa kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar 19 ga wata Oktoba 2023.

Ya ce yayin da ‘yan sanda suke gudanar da bincike sun gano cewa matashin ya sace tarin doya ne a wata gona mallakin makarantar sikandiren Dutse Alhaji.

Chinedu, ya kara da cewa wanda ake tuhumar yayi bayani kan cewa ya saci doyar ne da niyyar sayar da ita daga bisani aka kama shi.

Ogada, ya ce wannan laifi da matashin ya aikata ya sabawa sashi na 348 da 287 na kundin hukunce hukuncen penal code. Alkalin kotun, ya gargadi wanda ake tuhumar da ya kasance mai kyakkyawan hali nan gaba bayan kammala zaman gidan gyaran halin.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *