Inside Arewa Hausa

Labarun Hausa

Siyasa

Lauyoyin Aminu Ado Bayero sun janye daga shari’ar da suke da Gwamnatin Jihar Kano

Lauyoyin Aminu Ado Bayero sun janye daga shari’ar da suke da Gwamnatin Jihar Kano

Tun da farko lauyoyin sun roki kotun da ta dakata tunda sun daukaka kara akan hukuncin kotun na farko inda ta ayyana cewar Aminu Ado Bayero kada ya sake ayyana kansa a matsayin sarkin kano.

A zaman kotun na yau kotun ta yi kwarya-kwaryar hukunci inda bayyana cewar baza ta dakata ba sakamokon rashin gamsassun hujjoji.

Daga nan ne lauyoyin suka roki kotun da ta ɗaga musu zuwa wani lokaci dan su yi nazari, akan wasu takardu da masu kara suka basu jiya da yamma, kotun ta bayyana cewar bazata ɗaga musu ba tunda tun jiya aka basu takardun ya kamata ace sun yi nazari akansu.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *