Inside Arewa Hausa

Labarun Hausa

Labarai

ALHAMDULILLAH: Kaftin Ahmed Musa MON Ya Cika Alkawari, Ya Siya Wa Baba Karkuzu Gida Da Kyautar 500KKaftin din Super Eagles Ahmed Musa ya cika alkawarin da yayi na siyawa Mallam Abdullahi Shu’aibu wanda aka fi sani da Karkuzu Na Bodara gida biyo bayan hira da aka yi da da dattijon yana neman tallafin jama’a bayan makanta da ta same shi.

Bayan, haka, bayin Allah masu taro da sisi sun tallafawa Baba Karkuzu da zunzurutun kudi da ya kai Naira miliyan 2 da motsi.

Gidan ya kunshi dakuna “safe contain” guda 2 da “single” 3 da “kitchen” da bayan gida.

Saboda farin ciki da irin tallafin da ya samu, Karkuzu ya kasa rike farin cikin shi yayin da ake mika mishi takaddun gida inda ya fashe da kukan dadi tare da addu’o’in alkhairi ga bayin Allah da suka shiga lamarin shi. Karkuzu yayi godiya ga dukkan wadanda suka tallafa mishi tare da addu’o’i da dukiyar su.

Ga Mallam Abdullahi Karkuzu nan ya karbi takaddun gida tare da iyalansa. Ga Kuma hoton gidan nan da takaddun gidan nan an damka mishi.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *