Gwamnati Ta Rufe Makarantu Bayan Cutar Diphtheria Ta Kashe Dalibai 5 A Bauchi
Dalibai biyar sun mutu sanadiyyar wata cuta da ake zargin ta Diphtheria a Karamar Hukumar Jama’are da ke Jihar Bauchi.
Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar, Dokta Rilwanu Mohammed ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Bauchi ranar Laraba.
Ya kuma ce an dauki samfurin mutum 28 a Karamar Hukumar, inda biyu daga ciki aka tabbatar da sun kamu da ita, inda ya ce za su tashi tsaye wajen dakile yaduwarta.
Shugaban ya bayyana bullar cutar a matsayin abin damuwa, kuma yanzu haka za a ci gaba da bincike domin tabbatar da ko cutar ce ta kashe su.
Ya kuma ce za a bayar da allurar rigakafi domin kare ci gaba da yaduwarta. Ya kuma ce duk makarantar da aka samu rahoton bullar cutar a Jihar, za a rufe ta.