Inside Arewa Hausa

Labarun Hausa

Labarai Matsalar Tsaro

Fintiri Ya Sanya Dokar Hana fita Awa 24 A Adamawa

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, ya kafa dokar hana fita na tsawon awa 24 a jihar, biyo bayan fasa Ma’adanar ajiye abinci da matasa ke ci gaba da aiwatarwa.

Cikin wata sanarwar manema labarai da jimi’in yada labaran gwamnan Humwashi Wonosikou, ya aikewa manema labarai, tace dokar ta fara aiki nan take.

Ta ci gaba da cewa “abubuwan da matasan ke yi ya munana, da haifar da hargitsi, kai hare-hare ga jama’a, tsayar da harkokin yau da kullum, dama sace-sace a Yola fadar jihar.

“An kafa dokar hana fita, ba’a bukatar ganin kowani mutum a waje, wanda ba wani muhimmin yake gudanarwa ba, babu shiga ko fita daga jihar.

Sanarwar ta kuma roke jama’a da su bi doka da oda, tace duk wanda ya karya dokar zai gamu da fushin jami’an tsaro.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *