Inside Arewa Hausa

Labarun Hausa

Labarai

Amarya Ta Shiga Hannun ‘Yansanda Bayan Yanke Mazakutar Mijinta A Katsina

Wata Amarya mai suna Nana ‘yar shekara 17 ta yanke mazakutar mijinta a daren farko na aurensu a kauyen ‘yar Kasuwa da ke karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina.

A wani rahoto da DCL Hausa ta rahoto, ta ce, mijin mai suna Malam Abubakar tun kafin aure ya dade yana zuwa zance wurin amaryar ta shi har zuwa lokacin da yayi nasarar aurenta suka tare a daren Lahadin da ta gabata, a wayewar Litinin ne Nana tasa reza ta yanke masa mazakuta.

Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a san dalilin da ya haddasa rikici a tsakaninsu ba wanda ya kai ga Nana ta yanke wa mijinta Abubakar mazakuta. Amma dai, mijin na asibitin Kwandala na garin Malumfashi yana jinya.

Sai dai bayanan da DCL Hausa ta tattara sun ce, yanzu haka Amarya Nana ta shiga hannun jami’an ‘yansanda.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *