Inside Arewa Hausa

Labarun Hausa

Labarai Siyasa

’Yan Bindiga Sun Harbe Sojoji 7 Da Manoma 22 A Zamfara

Akalla sojoji bakwai da manoma 22 ne aka kashe yayin wani artabu tsakanin dakarun rundunar tsaro ta Operation Hadarin Daji da ’yan bindiga a Jihar Zamfara.

An yi ba-ta-kashin ne a kusa da garin Kangon Garucci da ke gundumar Dangulbi a Karamar Hukumar Marun Jihar ta Zamfara. A cewar wani mazaunin yankin mai suna Sani Baba, “Yayin da aka kashe wasu daga cikin manoman lokacin da suke tsaka da aiki a gonakinsu, wasu kuma sun rasu ne lokacin da sojojin ke musayar wuta da ’yan ta’addan.

“Wani dan bindiga Ali Kawajo da Damina da wani mai suna Black ne suka jagoranci kai harin. “Shi dama Black ya yi kaurin suna a yankin wajen dora wa manoma haraji, duk ya bi ya gama talauta su daman,” in ji Sani.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton duk kokarin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin rundunar Operation Hadin Kai, Kyaftin Ibrahim Yahaya, a kan lamarin, ya ci tura. A wani labarin kuma, wasu dakarun na rundunar tare da hadin gwiwar sojojin rundunar FOB da aka girke a Wanke da ke Karamar Hukumar Gusau, sun kashe ’yan bindiga akalla shida.

Sojojin sun samu nasarar ce bayan wani kwanton bauna da suka yi wa maharan a kan hanyarsu ta zuwa wani garin. Kazalika, sun kuma samu nasarar kwace wata bindiga da harsasai da kuma wani babur daga ’yan bindigar da ke kokarin tserewa.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *