Inside Arewa Hausa

Labarun Hausa

Labarai

Wata Yarinya Ta Rasa Ranta Bayan Wani Malami Ya Ci Zarafinta A Kano



Mahaifin wata yarinya ’yar shekara 11 da ta rasa ranta bayan da wani malami ya yi mata fyade a Jihar Kano ya roki gwamnati da hukumomin kare hakkin dan Adam su kwato masa hakkin ’yarsa.

Mahaifin ya bayyana cewa ’yar tasa ta rasu ne sakamakon matsalar da ta samu a lokacin fyaden.

Malam Dauda Musa, da ke Karamar Hukumar Dala ya bayyana cewa bayan an yi wa ’yarsa fyade ne suka kai ta asibiti inda likitoci suka tabbatar da cewa ta samu munanan raunuka a al’aurarta sakamakon munin lamarin.

Ya ci gaba da cewa kusan watanni hudu yarinyar ba ta iya yin fitsari cikin sauki, don haka suka yawaita kai ta asibiti har a makon jiya da ta rasu.

Don haka ya yi kira ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf; da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero; da kuma Kungiyoyin kare hakkin dan Adam da duk wanda abin ya shafa da su taimaka musu wajen ganin an kwato hakkin marigayiyar.

Majiyar Kakaki24 ta bayyana cewa, an kama wanda ake zargin, wanda malami ne a unguwar Dandinshe Quarters da ke karamar hukumar Dala.

Daga bisani kuma an gurfanar da shi a gaban kotu mai lamba 47 da ke yankin Nomans Land, a Kano, inda alkali ya da umarnin a ci gaba da tsare shi tare da dage shari’ar zuwa ranar 29 ga watan Afrilun nan da muke ciki domin ci gaba da sauraren karar

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *