NNPCL ya ayyana dokar ta-ɓaci a harkokin man fetur na Najeriya – Kyari
Mele Kyari
Kamfanin man fetur na gwamnatin Najeriya NNPCL ya ce ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkokin haƙowa da kuma fitar da ɗanyen mai daga ƙasar.
Shugaban kamfanin, Mele Kyari, ya ce sun ɗauki matakin ne da zimmar haɓaka yawan man da ake haƙowa, yana mai cewa bincikensu ya nuna “Najeriya za ta iya haƙo fiye da ganga miliyan biyu duk rana”.
“Mun ayyana yaƙi ne a kan ƙalubalen da muke fuskanta a harkokin haƙo fetur. Mun shaida wa abokan hulɗarmu, muna da kayan aikin aiwatar da hakan kuma mun san abin da za mu yi,” a cewarsa yayin da yake magana a taron masu ruwa da tsaki a harkar mai ta Najeriya ranar Talata a Abuja.
Ya ƙara da cewa “yaƙin zai taimaka wa NNPCL da abokan hulɗarsa kawo ƙarshen duka matsaloli domin cigaba da haƙowa da sayar da man ba tare da wani tsaiko ba”.
Da yake magana kan motoci masu amfani da iskar gas na CNG, Kyari ya ce tuni kamfanin ya gina tashoshin CNG ɗin da dama, inda za su ƙaddamar da 12 daga ciki a Legas ranar Alhamis mai zuwa.