Inside Arewa Hausa

Labarun Hausa

Labarai Siyasa

Gwamnan Sakkwato Ya Tube Rawanin Wasu Hakimai 15 a Jihar



Gwamnatin Sakkwato ta sallami hakimai 15 bisa zargin su da taimakawa rashin tsaro, satar filaye da sauran laifuka.

An sallami hakimai 9 daga mukamansu bisa zargin su da rashin biyayya da taimakon rashin tsaro da satar filaye da kuma karkatar da dukiyar jama’a da rashin da’a.

Wadanda aka sallama su hada da hakiman Uguwar Lalle, Yabo, Wamakko, Tulluwa, llela, Dogon Daji, Kebbe, Alkammu, da kuma Hakimin Gyawa.

Gwamnatin jihar ta kuma sauke wasu hakimai shida da tsohuwar gwamnatin jihar ta nada.

Abubakar Bawa, Sakataren yada labarai na Gwamna Ahmed Aliyu, ya bayyana cewa an sauke hakiman shida ne saboda yadda aka nada su ba bisa ga ka’ida ba, sannan da yawa mutanensu sun ki amincewa dasu.

Hakiman sun hada da hakimin Marafan Tangaza, Sarkin Gabas Kalambaina, Bunun Gongono, Sarkin Kudun ’Yar Tsakkuwa, da kuma Sarkin Tambuwal da Sarkin Yamman Torankavwa.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *