Inside Arewa Hausa

Labarun Hausa

Labarai Siyasa

Bincike Ya Nuna Ayyukan Layin Dogo Da Dama A Fadin Najeriya Sun Tsaya Cak

Ayyukan layin dogo da dama na sama da naira tiriliyan 16 a fadin kasar nan sun tsaya cak saboda rashin kudi, kamar yadda wani binciken jaridar Daily Trust ya nuna.

Wannan ci gaban yana barazana ga shirin gwamnatin tarayya na sabunta hanyoyin jirgin kasa da aka tsara don haɗa dukkan jihohin tarayyar.

Ayyukan sun hada da titin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano, aikin layin dogo daga Legas zuwa Calabar, aikin gyaran layin gabas (Port Harcourt-Maiduguri) da aikin layin dogo na Kano zuwa Maradi.

Dukkan ayyukan an hada su ne a cikin taswirar layin dogo na tsawon shekaru 25 da aka kaddamar a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo wanda zai kare a shekarar 2025.

Aikin layin dogo na gabar teku daga Legas zuwa Calabar wanda aka shafe kusan shekaru 20 ana gudanar da shi a shekarar 2021 ne Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da shi a lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari.

Idan dai za a iya tunawa, a shekarar 2016, kasashen China da Najeriya sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta sama da dala biliyan 11 don gina layin dogo a gabar teku da za a fara kafin karshen shekarar 2018.

Yayin da aikin ya shirince, gwamnatin tarayya a lokaci guda ta kaddamar da aikin titin Legas zuwa Ibadan mai nisan kilomita 157 tare da kammala shi cikin lokaci mai tsawo.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *