Inside Arewa Hausa

Labarun Hausa

Harkar Lafiya Labarai

Ɗabi’ar Da Ke Saurin Janyo Cutar Basir

Ɗabi’ar Da Ke Saurin Janyo Cutar Basir

 

Bayan ƙaranta shan ruwa, ƙaranta cin harza ko datsar abinci akwai ƙarin ɗabi’ar da ke saurin janyo cutar basir.

 

Wannan ɗabi’ar ita ce yin buris ko yin watsi da yin bayan gida a daidai lokacin da aka ji shi tare da jinkirta shi zuwa wani lokaci.

 

Wannan ɗabi’a tana sa bayan gida ya ƙaya yin tauri sosai wanda hakan ke ƙara wahalar yunƙuri yayin yin bayan gidan. Wahalar yunƙuri fiye da ƙima yana takura jijiyoyin jini a cikin dubura har jijiyoyin jinin su kumbura.

 

Dalilin da ke sa bayan gidan ya ƙara tauri yana da alaƙa da tsawaitar zamansa a cikin babban hanji ko dubura fiye da yadda aikin jiki ya tsara. A wannan lokaci babban hanji yana ƙara tsotse ruwan da ke cikin bayan gidan yanayin da ke sa bayan gidan ya ƙara tauri.

 

Zaɓi yin bayan gida a lokacin da ka ji shi domin kauce wa basir ko ta’azzararsa.

 

Duba ƙarin hanyoyi shida domin kiyaye basir cikin sauƙi a nan:

© Physiotherapy Hausa

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *