Inside Arewa Hausa

Labarun Hausa

Labarai Siyasa

Kotu ta Yanke Hukunci kan Dambarwar Masarautar Kano har illa Masha Allah



Babbar kotun jihar Kano ta haramtawa Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero da sarakunan Karaye, Gaya, Rano da kuma Bichi ayyana kansu a matsayin sarakuna har illa Masha Allah

Kuma Babbar Kotu Ta Bada Sabon Umarni ga Aminu Ado Bayero da Sauran Sarakunan 4 da Aka Tsige da su Tattara duk kayan Sarrauta da ke hannun su su mika ka wa Gwabnatin Jihar ko Sarki Sanusi

Babbar kotun jihar Kano ta tura umarni ga sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna huɗu da Gwamna Abba Kabir ya tsige Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta umarci Aminu da sauran sarakunan su miƙa dukkan kayan gidan sarauta ga gwamnatin jihar Kano Haka nan kuma ta haramtawa sarakunan guda biyar ci gaba da bayyana kansu a matsayin sarakunan Bichi, Rano, Ƙaraye da Gaya

Babbar kotun jihar Kano ta bayar da sabon umarni ga Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna huɗu da aka tube wa rawanin sarauta. Kotun ta umarci sarakunan guda biyar su tattara dukkan kayan sarauta da ke hannunsu, su miƙawa gwamnatin jihar Kano ko kuma Sarki na 16, Muhammadu Sanusi.

Kotu ta hana Aminu amsa sunan Sarki

Idan ba ku manta ba mun kawo muku rahoton cewa kotun ta hana Aminu Ado da sauran sarakuna huɗu amsa sunan sarakuna a jihar Kano.

Mai shari’a Amina Aliyu ce ta yanke wannan hukunci ranar Litinin, 15 ga watan Yuli a karar da gwamnatin jihar Kano ta shigar gabanta.
Ta kuma haramtawa duka waɗanda sarakunan biyar suka naɗa a wata sarauta daga nuna kansu a matsayin sarakuna, rahoton Channels tv.

Tun farko gwamnatin Kano ta umurci Aminu Ado da sarakunan da ta tuɓe su bar masarautunsu cikin sa’o’i 48 daga lokacin da aka tsige su. Bisa haka ne mai shari’a Amina ta umarci sarakunan su mika dukkan kadarorin gidan sarauta da ke hannunsu ga gwamnatin Kano ko sarki na 16 Muhammadu Sanusi II.

Kwankwaso ya faɗi dalilin tuɓe Sarkin Kano

A wani rahoton kuma kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana musabbabin tuge sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero. Kwankwaso ya ce Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya dauki matakin ne saboda cika alkawuran da ya daukar al’umma a lokacin yaƙin neman zaɓe

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *