Wata babbar kotu a jihar Kano ta ɗage zamanta a shari’ar da majalisar dokokin jihar da gwamnatin jihar suka shigar inda suke neman sarkin Kano na goma sha biyar ya daina ayyana kansa a matsayin sarkin Kano.
Yau ne kotun ta shirya sauraron gundarin shari’ar amma kasancewar ɓangaren masu ƙarar basu kammala mayar da martani ga buƙatun da masu kariya suka gabatar ba aka ɗage zaman.
Wannan na zuwa ne ƴan kwanaki bayan babbar kotun tarayya ta yi hukuncin cewa dokar da ta rushe masarautu a jihar na nan daram amma kuma ta soke aiwatar da dokar wadda gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.
Babbar kotun ta shirya sauraron ɓangarorin biyu, inda aka yi tsammanin kowanne zai gabatar da hujjoji da kuma kariya a dambarwar shari’ar masarautar Kano da ke ci gaba da ɗaukar hankali.
To sai dai a yau ma kotun ta gaza jin jigon shari’ar da majalisar dokokin Kano ta shigar da ƙarar ‘yan sanda da sojoji da hukumar tsrao ta farin kaya DSS da civil defence da kuma sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero.
Ɗaya daga cikin lauyoyin Sarki Aminu Ado, Bar Abdulrazak A. Ahmad ya shaida wa BBC cewa tun jiya sun shigar da wasu buƙatu gaban kotun.
Ya ƙara da cewa buƙatun sun haɗa da neman kotu ta ajiye shari’ar tun da “a iya fahimtarmu, kotu tana da sha’awa a ciki, da neman kotu ta saka mutanen da ba sa ciki a shari’ar, sannan a kira shaidu a yi masu tambayoyi da kuma buƙatar kowa ya gabatar da jawabi ta yadda za a ɗauki shaida tiryan-turyan.” kamar yadda ya yi bayani.
To sai dai ɓangaren majalisa da gwamnatin Kano waɗanda suka shigar da ƙarar sun soki waɗannan buƙatu. Bar Ibrahim Wangida na cikin lauyoyin majalisar, ya ce a jiya suka karɓi takardun buƙatun ɓangaren waɗanda ake ƙarar.
A cewarsa, “abin da suka sani shi ne majalisa ta yi doka, gwamna ya sa mata hannu saboda haka ta zama doka, kuma kotu ce kaɗai za ta iya fassara wannan doka shi ya sa muka taho kotu ta fassara.”
Mai shari’a Amina Adamu ta ce sai ranar huɗu ga watan da muke ciki ne za ta zauna don sauraron shari’ar.
Wannan dai shi ne kusan karo na uku da babbar kotun jihar ke zama don sauraron gundarin shari’ar amma ana ɗage zaman.
A gefe guda kuma, babbar kotun tarayya da ke zama a Kano ƙarƙashi mai shari’a Amobeda Simon, ita ma ta ɗage zamanta zuwa ranar Litinin takwas ga wata da muke ciki, don yin wani ƙwarya-ƙwaryar hukunci kan buƙatar ɓangaren gwamnati ta neman a jingine ci gaba da sauraron ƙarar da Aminu Babba ya shigar wadda Mai shari’a AM Liman ya yi hukunci a watan jiya, har sai an saurari ɗaukaka ƙarar da suka yi.
Inside Arewa Hausa
Labarun Hausa