Inside Arewa Hausa

Labarun Hausa

Matsalar Tsaro

Ƴan bindiga sun bindige malamin Jami’ar Dutsin-Ma, sun arce da ‘ya’yan saTabbatattun bayanai daga Katsina sun nuna ‘yan bindiga sun afka garin Dutsinma, sun bindige ɗaya daga cikin malaman Jami’ar Tarayya ta Dutsinma (FUDMA).
Maharan sun bindige Dakta Tiri Gyang-David a gidan da ke Rukunin Gidaje na Yarima Quaters, Low Cost Estate, Dutsinma da misalin ƙarfe 1:30 na dare a jiya Litinin.

Gidan Talbijin na Channels da jaridar DCL Hausa sun ce ‘yan ta’addar sun kuma tafi da ‘ya’yan malamin jami’ar guda biyu.

Sai dai kuma ba a tantance shin maza ne ko mata ne aka tafi da su ɗin ba.

‘Yan bindiga da ba a kai ga tantance adadin su ba ya zuwa wannan lokaci sun kutsa kai cikin garin Dutsinma na Jihar Katsina, inda suka harbe wani malamin Jami’ar tarayya ta FUDMA da aka bayyana sunan sa da Dakta Tiri Gyang-David.

Majiya ta ce kuma maharan sun kuma yi awon-gaba da ‘ya’yan sa biyu da ba a sanar da jinsin su ba, wato maza ne ko mata, ko kuma mace da namiji.

Lamarin ya faru a daren Litinin wayewar Talata da misalin ƙarfe 1:30 na dare.

Majiyar ta ce yanzu haka gawar Dakta Tiri Gyang-David da ke koyarwa a Sashen Tattalin Arziki na Fannin Noma, na can a Babban Asibitin garin Dutsinma Jihar Katsina.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar Katsina ASP Aliyu Abubakar Sadiq ya tabbatar wa gidan talbijin na Channels afkuwar lamarin, kuma ya ce ana nan ana ƙoƙarin kuɓutar da waɗanda aka arce da su ɗin

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *