Inside Arewa Hausa

Labarun Hausa

Labarai Siyasa

Gwamna Uba Sani ya mayar da Sarkin da El-Rufa’i ya sauke



Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya tabbatar da mayar da Cif Jonathan Zamuna a matsayin babban Sarkin Piriga a karamar hukumar Lere Ya kuma jaddada muhimmiyar rawar da cibiyar ta gargajiya ke takawa wajen samar da zaman lafiya ba a jihar Kaduna kadai ba har ma da kasa baki daya.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya tsige Cif Jonathan Zamuna daga mukaminsa a ranar 22 ga Mayu, 2023, daf da karewar wa’adi na biyu na Gwamnan sa.

A zaman da ya yi da majalisar sarakunan jihar a yau Alhamis, 4 ga watan Yuli, Gwamnan ya jaddada muhimmancin maido da Sarkin gargajiyar. Ya bayyana irin muhimmiyar rawar da ubannin sarauta suke takawa wajen inganta shugabanci na gari da tabbatar da tsaron al’ummarsu, inda ya jaddada cewa hada kai da su na da matukar muhimmanci a dukkan matakan Gwamnati.

“A cikin shekara guda da muka yi kan mulki, mun dauki manyan masu ruwa da tsaki a kan manufofinmu, kuma wannan ya hada da muhimman ayyuka da cibiyarmu ta gargajiya. Don haka kofofinmu a bude suke don ci gaba da huldar mu a kan al’amuran ci gaba da tsaron jiharmu.

“Bugu da kari kuma, a matsayin shaida na na tabbatar da bin doka da oda, ina so in sanar da ku aniyarmu ta yin aiki da hukuncin da kotu ta yanke a ranar 10 ga watan Yuni, 2024, na maido da shugaban Piriga, a karamar hukumar Lere. Mai Martaba, Jonathan Zamuna Zuwa stool dinsa.”

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *