Inside Arewa Hausa

Labarun Hausa

Labarai Siyasa

Kalubalen da ake fuskanta A Najeriya Yasamu Asali ne Daga Gwamnatocin da suka Gabata

Kalubalen da ake fuskanta A Najeriya Yasamu Asali ne Daga Gwamnatocin da suka Gabata

Muhammad Sanusi II, Sarkin Kano, ya bayyana cewa Najeriya na fuskantar kalubale da ta gada. Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar gwamnatin jihar Kano a fadarsa ta Gidan Dabo ranar Alhamis.

Sanusi ya jaddada cewa al’ummar kasar ba za su iya ci gaba da kokawa kan wadannan kalubale ba, Yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa za a iya shawo kan su da tsayin daka da kuma halin kwarai.

“Ina da yakinin cewa al’ummar kasa baki daya na fuskantar kalubalen da suka gada, sannan kuma jihohi suma suna fuskantar kalubalen da suka gada. Amma mafita ba ita ce yin kukan abin da ya faru a baya ba,

“Ina da yakinin cewa al’ummar Kano tare da tarihinmu, tsayin daka, da dabi’unmu, za su iya shawo kan wadannan kalubale, ya zama wajibi a samar da shugabanci don tsara yadda jama’a za su san cewa za su iya tsayawa da kafafunsu ba wai sun durkusa ba. ” in ji shi.

Da yake yabawa gwamnatin jihar kan manufofinta na ilimi, fansho, da kuma biyan kudaden gratuti, Sarkin ya tabbatar wa da tawagar cewa kofarsa a bude take domin neman shawarwari da tuntubar juna. Ya kara da cewa masarautar za ta ci gaba da yi wa Gwamnatin jihar addu’ar samun nasara.

Tun da farko kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Baba Halilu Dantiye, ya shaida wa Sarkin cewa tawagar ta je fadar ne domin nuna irin nasarorin da gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta samu a cikin shekarar da ta gabata. Ya kuma ce sun kai ziyarar ne domin neman gudunmawar Sarkin wajen ciyar da jihar gaba.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *