Inside Arewa Hausa

Labarun Hausa

Labarai Siyasa

Gwamnatin jihar Sokoto tace bisa tsarin mulki, Sarkin Musulmi ba shi da ikon nada kowa

Gwamnatin jihar Sokoto tace bisa tsarin mulki, Sarkin Musulmi ba shi da ikon nada kowa.

Kwamishinan Shari’a na jahar Barista Nasiru Binji ne ya sanarda hakan yau Talata a wajen taron jin ra’ayin jama’a kan dokar kananan hukumomi da masarautu ta Sokoto 2008.

Binji yace dokar da ake da ita a jihar ta sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Yace sashe na 76(2) na dokar ya sabawa sashe na 5(2) na kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

“Sashi na 5 (2) na kundin tsarin mulkin kasa ya nuna cewa ikon zartarwa na nadawa a jihar yana hannun Gwamna ne kai tsaye ko ta hannun mataimakinsa ko kwamishinoni ko duk wani wakilin gwamnati da Gwamna ya ba shi.

Don haka babu wani ikon da aka bai wa Majalisar Sarkin Musulmi ta yin nadi.

Sashi na 76(2) na dokar karamar hukumar Sokoto da masarautar Sokoto ya baiwa Majalisar Sarkin Musulmi ikon nada Hakimmai da Uwayen Ƙasa a jihar amma tare da amincewar gwamna mai ci.

“Don haka sashin bai dace da kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima ba, saboda haka ba zai iya tsayawa ba. Domin kuwa ikon nadi shina a bangaren zartaswa kuma su waye suke gudanar da mulki, shin ba Gwamna ba ne? Wannan shi ne dalilin gyara. Domin gyara kuskuren da aka yi a baya,” inji shi.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *