Inside Arewa Hausa

Labarun Hausa

Siyasa

An buƙaci gwamnatin tarayya da ta Koma kan tsarin su Sardauna da Awolowo da Azikiwe, da kuma Ɓalewa



An buƙaci Gwamnatin Tarayya ta sake duba tsarin Mulkin Alhaji Abubakar Tafawa Balewa, da Dr. Nnamdi Azikiwe, da Cif Obafemi Awolowo, da Sir Ahmadu Bello da sauran magabata domin shawo kan ƙalubalen zamantakewa da siyasa da kasar ke fuskanta a halin yanzu.

Babban kodinetan kungiyar National Unity Pathfinders (NUP) na kasa Ambasada Sixtus Obinna Nwoke da Sakataren ta na ƙasa Saleh Alhassan Kubah ne suka yi wannan kiran a Abuja a wajen taron kaddamar da wani kwamiti na kungiyar.

Sun ce kalubalen da ake fuskanta a halin yanzu ba za a iya tsallake sa ba, har sai an yi duba kan tsare-tsare da abubuwan da Shugabannin yanzu suka gada na Mulkin adalci daga Shugabannin ƙasar da suka yi gwagwarmayar kafa kasar, suna mai cewa hakan zai taimaka wajen samar da mafita mai ɗorewa kan ƙalubalen.

Taron ya samu halartar jiga-jigan siyasa da tattalin arziki a duka shiyyoyin siyasar kasar nan shida.

Muna tunatar da al’umma irin namijin kokarin da magabatanmu na kwarai suka yi wajen ganin an samu hadin kai da wadata a Najeriya.

Abubuwan da suka gudanar ya zama kamar kira ne a gare mu domin ƙarasa aikin da ba su kammala ba na gina ƙasa, inda haɗin kai da zaman lafiya ya zama abinda suka fi baiwa fifiko.

A yau mun taru a matsayin masu neman wata hanya don tsara yadda za mu bada gudummawar mu domin cigaban Najeriya.

“Mun haɗa kai ne a kokarinmu na samar da Najeriya wacce ta dace da muradun kasar kamar yadda muke so. Muna hangen Najeriya za ta kasance bisa tafarkin haɗin kai da kuma sadaukarwa domin samawa ‘yan kasa jindadi da walwala,” inji Nwoke.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *