Dalibai sun shiga mawuyacin hali hana Adaidaita sahu hawa manyan titunan Kano

Dalibai ‘yan makaranta da sauran al’umma na ci gaba da kokawa kan irin mawuyacin halin sufuri da suka tsincin kan su, sakamakon dokar haramtawa Baburan Adaidaita Sahu bin wasu daga cikin manyan titunan jihar Kano a ranar Laraba.

A ziyarar da muka Kai daya daga cikin titunan na Gwarzo Road, a yankin Rijiyar Zaki, mun iske tarin fasinjoji, suna jiran dogwayen motocin na gwamnatin, wasu kuma sun gaji da jira suna tafiyar kasar, sabo da karancin motocin da kuma sharadin sai Wanda yake da ticket ne zai hau.

Hakan ya janyo a wasu lokutan ko an tare su a kan hanya ba sa tsayawa, domin daukar fasinja in dai ba’a madakatar su ba inda suke siyar da ticket din. Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Soron Dinki ya rawaito cewar, an sanya jami’an tsaro a wurare daban-daban, domin tabbatar d  direbobin Baburan Adaidaita Sahun sun bi dokar, lamarin da ya sanya ba a sami wani direban Adaidaita sahun da ya karya dokar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: