Amsoshin da Firaministan Birtaniya ya samu daga Buhari basu mishi daɗi ba

 

Fahimtar Abdulhadi Isa Ibrahim

 

Ba lallai gwamnatin Burtaniya (England) ta cigaba da kawance mai kyau da Nigeria ba, a fahimta ta, saboda amsoshin da shugaba Buhari ya bayar ma Prime Ministan Britannia wato Boris Johnson, na tabbata shugaba Buhari ya bada amsoshin ne cikin bacin rai ko kuma dama tuni yana kullace da Britannia akan wasu lamuran da suka shafi Nigeria.

Shugaba Buhari ya hadu da Boris Johnson jiya Al-Hamis a Rwanda, wajen taron Commonwealth, sun tattauna wanda da alama bata yi dadi ma Prime Ministan Britannia ba.

 

Boris Johnson yayi tayi ma shugaba Buhari, yace:

“Zamu taimaka ma kasar ka akan batun tsaro, da kawo karshen matsalar kashe kashe a kasar ka Nigeria”.

Sai Buhari yace:

“A’a da kun taimaka ma wasu da yafi, ba mu ba, ku kai taimakon ku wani waje yafi ku kawo Nigeria”.

Boris Johnson yace, kamar ina kake nufi.

Shugaba Buhari yace:

“Kamar Libya mana, idan kuna son shawo kan matsalar tsaro a yankin kasashen Sahel to ku fara dakile matsalar Libya, ana dakile can toh an gama da nan, dan haka ku fara kai taimako can tukun”.

 

Boris Johnson yace:

“Toh ya batun tazarce, zaka sake neman mulkin Nigeria idan aka baka dama?”.

Shugaba Buhari yace:

“Allah ya sauwaka, bana fata, bana burin sake zama a mulkin kasar koda rana daya ne bayan wa’adi na ya cika”.

“Kaje ka duba akwai wanda yayi mulki kafin ni (Obasanjo) yaso yayi tazarce (a 2007) yaya ya wanke? bai ‘kare lafiya ba, toh ni bana bukatan cigaba da mulkin ne ma gaba daya, idan kaje Nigeria zaka ga nayi nisa wajen shirye shiryen mika mulki zuwa yanzu, bana bukatan cigaba da mulki ko kadan”.

 

Boris Johnson ya sake cewa:

“Mun samu rahotan dake cewa gwamnatin ka tana kuntata ma Nnamdi Kanu, mai fafutukar kafa kasar Biafra, an daure shi, baku bashi damar ganawa da Lauyoyin sa da Likitoci domin duba lafiyar sa”.

Shugaba Buhari yace:

“Ba gaskiya bane wannan rahotan, Nnamdi Kanu yayi ta fadin maganganu da yaga dama akan Nigeria a lokacin da yake cikin kasar ku (Britannia), yana ganin yana da iko da kariya”.

 

“Shiyasa muka kafa masa tarko, duk ranar da ya fita daga kasar ku sai an kama shi, kowace kasa yaje a duniya, kuma haka aka yi, nasa an rike shi kuma za a masa hukunci dai dai da dokokin Nigeria bisa laifin sa”.

“Muna bashi damar ganawa da Lauyoyi akan doka ba haka kawai ba, haka ma Likitoci, dan haka babu maganar mun tauye hakkin sa”.

 

Boris Johnson:

Shugaba Buhari nagode.

Buhari:

Nima nagode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: