Wani Dattijo Ya Cire Rufin Gidansa, Domin Ya Sayar Da kwanon Don Ya Biya Wa Ɗansa Kuɗin-Fansa

DAGA Ibrahim M. Bawa

Wani Dattijo mai suna Malam Sa’idu da ke a garin Faskari a yayin da yake ƙoƙarin cire kwanon gidansa ya sayar don biyan N100, 000 kuɗin fansar ɗansa da aka yi garkuwa da shi.

Rahotanni sun ruwaito cewa, tsohon da bai da cin yau, balantana na gobe, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shi a garin Faskari, ‘ya’yansa matasa suka haɗa kuɗin fansa suka kai naira dubu N50, 000, amma sai suka saki tsohon suka riƙe yaron nasa, daga bisani suka nemi karin naira N100, 000 kuɗin fansar yaron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: