Ɗan Shekara 25 Ya Ba Da Kwangilar Kashe Mahaifinsa Akan N110k Saboda Ya Gaji DukiyarsaDAGA Aliyu Adamu Tsiga

Rundunar ƴan sandan jihar Neja ta kama wani mutum mai suna Abubakar Mohammed Buba mai shekaru 25 da haihuwa da laifin hayar wani mutum don ya kashe mahaifinsa mai shekaru 52, domin ya ga ji kadarorinsa.

Kakakin ƴan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun ya ce an kama Abubakar na Gidan Madara a yankin Chanchaga, Minna a ranar 29 ga watan Disamba.

Jami’an ƴan sandan da ke aiki da sashin Chanchaga ne suka kama shi. Abubakar Buba mai shekaru 25 a duniya, ana tuhumarsa da laifin haɗa baki da wani don akashe mahaifinsa, Alhaji Mohammed Buba.

An kashe Alhaji Buba a gidansa da ke Korokpan, ƙaramar hukumar Paikoro a ranar 13 ga Oktoba, 2021. Yayin da ake yi masa tambayoyi, ɗan nasa ya amsa cewa ya haɗa baki da wani mai suna Aliyu Mohammed na Chanchaga don a kashe mahaifin nasa.

Daga baya ya jagoranci jami’an ƴan sanda zuwa Tagwai-Dam inda aka jefar da gawar mahaifinsa, Alhaji Buba bayan an yanka shi, aka cusa gawar a cikin buhu.

Abubakar ya ƙara da cewa ya biya Naira 110,000 ga wanda ya yi gudun hijira Aliyu. Da farko ya biya N50,000 inda daga bisani ya sake bashi cikon N60,000 bayan ya kammala kisan. Ya ce ya sayar da kadarorin mahaifinsa da ya mutu ne domin a samu daidaito.

Ƴan sanda sun ce suna ƙoƙarin cafke ɗan bindigan mai suna Aliyu Mohammed da ya tsere. A halin yanzu, an mayar da shari’ar zuwa SCID Minna

Leave a Reply

Your email address will not be published.