Zaa Rataye Wanda Ya Kashe Maƙocin Sa A Kano

Duk da dai wanda aka yankewa hukuncin yana da damar sake daukaka karar neman sabon hukunci a kotun gaba nan da kwanaki Talatin.
Babbar kotun jihar Kano da ke zaune a Milla Road ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani mai suna Balarabe Ahmad bayan ta same shi da aikata kisan kai a kan maƙocinsa kamar yadda rahotan ya riske mu.
Alƙalin yace hukuncin da aka yankewa mutumin sashi ne 221 na Panel Code.
Mai Shari’a Nasiru Saminu, Yayin gabatar da ƙararar an bayyana wa kotu cewar mutumin sun sami saɓani da maƙocinsa lamarin da ya kai ga ya caka masa wuƙar har lahira kuma dukkannin shedu sun tabbatar da haka.
A saboda haka ne ma Kotun ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar sargafe.

Leave a Reply

Your email address will not be published.