Kotu Ta Tabbatar Da Cewa A Shirye Najeriya Take Ta Yaƙi Ƴan bindiga ~Malami

Hukuncin Babbar Kotun Da Ta Ayyana Ƴan Bindiga A Matsayin Ta’adda A Abuja Ya Tabbatar Da Cewa A Shirye Najeriya Take Ta Yaƙi Ƴan bindiga ~Ministan Shari’a Ya Fadawa Al’umma.

 

Babban Lauyan Tarayya, kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya ce a ranar Juma’a sanarwar da kotu ta bayar kan ƴan bindiga ya tabbatar da kudirin gwamnatin tarayya na yaki da ƴan bindiga a Najeriya.

 

Ministan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Umar Gwandu ya fitar a Abuja.

 

Ya yi wannan tsokaci ne a kan matakin da babbar kotun tarayya ta ɗauka na ayyana ƴan bindiga a matsayin ƴan ta’adda a Najeriya.

 

Mai shari’a Taiwo Taiwo, wanda ya bayyana hakan a hukuncin da ya yanke kan tsohuwar ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar, ya bayyana cewa ayyukan kungiyoyin ƴan bindiga da ƴan Ta’adda a Najeriya sun zama ayyukan ta’addanci.

 

Alkalin ya kuma haramta ayyukan kungiyoyin da sauran su a kasar tare da ayyana su a matsayin ƴan ta’adda.

 

Ministan ya jaddada cewa tuni gwamnatin tarayya ta fara daukar matakan da suka dace domin kawo karshen ayyukan masu aikata laifuka a Najeriya.

 

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Ci gaban da aka samu yana nuni ne ga kudirin gwamnatin tarayya na bin ka’idojin kasa da kasa wajen mutunta ka’idojin yaki da ta’addanci, kungiyoyin ƴan aware, tayar da kayar baya, da kuma ƴan bindiga a kasar nan.

 

“Akan wannan hukuncin kotu na ayyana ƴan bindiga a matsayin ƴan ta’adda, gwamnatin tarayyar Najeriya ta dauki kwakkwaran matakai na tinkarar duk wasu kungiyoyin ƴan ta’adda da masu daukar nauyinsu a kokarin da take na ganin an magance dimbin kalubalen rashin tsaro a kasar nan.

 

“Ofishin babban mai shari’a na tarayya da ministan shari’a tare da hadin gwiwar hukumomin gwamnati da suka hada da jami’an tsaro suna aiki tukuru don yin abin da ya dace don cin gajiyar wannan hukuncin.

 

“Gwamnati za ta fitar da sanarwar haramcin ba tare da bata lokaci ba.” Inji Ministan Shari’a

 

#insidearewa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: