Ayyana Ƴan Bindiga A Matsayin Ƴan ta’adda Ba Zai Kawo Ƙarshen Rashin Tsaro A Najeriya Ba ~Inji Sheikh Gumi

 

Malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce a ranar Juma’a shelanta ƴan bindiga a matsayin ƴan ta’adda ba zai kawo karshen rashin tsaro a kasar nan ba.

Mai shari’a Taiwo Taiwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Juma’ar da ta gabata ya bayyana ƴan bindiga da ke addabar yankin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya a matsayin ƴan ta’adda.

Gumi, wanda ya mayar da martani ga hukuncin a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Tukur Mamu, ya fitar a Kaduna, ya bayyana hukuncin kotun a matsayin yanke hukunci ne kawai da aka dauka domin biyan bukatar siyasa.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Ina ganin gwamnatin tarayya ta yi kasa a gwiwa wajen bata sunan wani sashe na kasar nan, a kafafen yada labarai wanda hakan ba zai yi wani amfani a aikace ba domin tun kafin ayyana su ana yaki da su a matsayin ƴan ta’adda.

“Don haka, kawai wannan wani abu ne wanda na yi imani cewa ba zai canza yanayin ƙasar nan ba. Idan za a iya tunawa kungiyar nan ta Indigenous People of Biafra (IPOB) ita ma an bayyana ta a matsayin kungiyar ta’addanci, sanarwar har ma da umarnin kotu ta goyi bayanta amma kamar yadda kuke gani, ko kasashen duniya ma ba su amince da ayyanawar gwamnatin tarayya game da IPOB ba. Don haka ayyanawar ta kasa yin tasiri ko cimma sakamakon da ake so.

“Ba a hana su yin balaguro zuwa wasu ƙasashe ba. Kasancewarsu ƴan kasa yana nan daram, ba a yi tir da shi ba. To wace irin ayyanawa ce haka? Ina fatan ƴan Najeriya da gaske ba za su dauki makiyaya a matsayin ƴan ta’adda ba amma su dauki laifin da wasu tsirarun daga cikinsu suke yi wa kan wadanda ba su ji ba ba su gani ba a matsayin ta’addanci, kamar yadda muke ganin kungiyar IPOB da hare-haren da suke kai wa jami’an tsaro da sauran ƴan Arewa a matsayin ta’addanci. Makiyaya ƴan bindiga kadan ne, idan ka bi ta yawansu.

“Ina fata wannan sanarwar ba za ta baiwa mutane lasisin ɗaukar makiyaya gaba daya a matsayin ƴan ta’adda da daukar doka a hannunsu a kansu ba. Domin haka zai haifar da ƙarin tashin hankali. Sanarwar ba za ta canza komai ba, ba za ta canza yanayin ba. Tuni sojoji suna ƴaki da su, amma haka bai hana su yin garkuwa da kisa ba. Sanarwar ba za ta kawo karshen cin zarafi da suke yi wa al’umma ba.

Rikicin Fulani matsala ce ta zamantakewa da tattalin arziki. Mun gani, mun yi hulɗa da su sosai. Muka fadawa gwamnatin tarayya mafita. Za a iya samun nasara ta hanyar haɗin gwiwa, tattaunawa, da adalci. Shi ya sa a yau an samu zaman lafiya a yankin Neja Delta domin gwamnati ta amince da abinda ake gaya mata na janyo su a jiki tare da yi musu gyara su da kuma ba su karfin gwiwa.

“Dole ne a samar da daidaito wajen rabon arzikin kasa a Najeriya kuma a yi adalci ga kowa da kowa.

“Fulani sun sha wahala sosai. Sun yi asarar halaltacciyar hanyar rayuwa, ina nufin shanunsu ta hanyar satar shanu da kwacen da jami’an tsaro ke yi. Dole ne a magance hakan a matsayin hanyar sulhu da haɗin kai na gaske. Yakamata suma su ji daɗin zama.” Inji Shi.

#insidearewa

Leave a Reply

Your email address will not be published.