Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sake Koma Hanyar Abuja Zuwa Kaduna Sun Yi Awon Gaba Da Mutane Da Dama

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sake Koma Hanyar Abuja Zuwa Kaduna Sun Yi Awon Gaba Da Mutane Da Dama.

 

Masu garkuwa da mutane sun koma hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin, inda suka yi awon gaba da matafiya da dama a karo na biyu cikin awanni 24.

 

Masu garkuwa da mutanen sun yi garkuwa da fasinjojin da ba a tantance adadinsu ba a ranar Lahadin da ta gabata tare da kashe wani fitaccen dan siyasar Zamfara, Sagir Hamidu.

 

Kafofin watsa labaru dai sun tattaro cewa masu garkuwa da mutanen sun koma kan babbar hanyar ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar Litinin, inda suka bude wuta kan masu ababen hawa.

 

Majiyoyi sun ce lamarin ya afku a kasa da kilomita biyar daga inda maharan suka gudanar da aikin a ranar Lahadi.

 

Lawan Sani, wani ganau da ya ratsa kan titin nan da nan bayan faruwar lamarin ya shaida wa Daily Nigeria cewa ya ga akalla motoci hudu da aka yi watsi da su dauke da fashe-fashe na gilashi da kuma tayoyin mota.

 

“An yi mugun hayaniya da firgici a kewayen yankin. Kusan nan take sojoji suka isa wurin amma ƴan bindigar sun kammala aikin cikin gaggawa cikin mintuna sannan suka bace cikin daji tare da mutane da dama.

 

“Na ga wata motar bas mai kujeru 18 mallakar Zamfara Mass Transit, Toyota Yaris, Volkswagen Golf da kuma wata mota guda daya ban iya tunawa da samfurin ta ba. An far wa motocin da harsasai tare da mutanen da ke cikin su ,” Mista Lawan ya kara da cewa.

 

#Insidearewa

Leave a Reply

Your email address will not be published.