Matashi ya mutu a hannun ƴan-vigilante bayan mahaifinsa ya kaishi ai masa hukunci

 

Wani matashi mai suna Haruna Auwala ya rasu a ofishin ƴan vigilante bayan da mahaifinsa, Auwala Ado ya kai shi a yi masa hukunci sabo da ya kangare.

 

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Kafin Gana da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu da ke Jihar Jigawa.

 

Tun da fari dai shi Auwala na zargin ɗansa da satar masara a gonar mutane, inda sakamakon ɓacin rai, sai ya kaishi ofishin ƴan vigilante da a ka fi sani da ƴan bulala domin a hukunta shi.

 

Bayan ya kai marigayin, sai ƴan bulala ɗin su ka hukunta shi ta hanyar bashi gwale-gwale inda daga nan ne sai jikinsa ya rikice har a ka garzaya da shi asibiti.

 

Bayan an kaishi asibiti ba da daɗewa ba ne sai kuwa Haruna ya ce ga garinku nan.

 

Kakakin Rundunar Ƴan sanda ta Jihar Jigawa, ASP Lawan Shisu Adam ya tabbatar da faruwar al’amarin.

 

Kakakin ya kuma tabbatar da cewa tuni su ka cafke mahaifin marigayin da kuma wani mutum guda ɗaya sannan za a faɗaɗa bincike.

 

Ya kuma yi kira ga iyaye da su riƙa yiwa ƴaƴansu hukunci mai sauƙi domin gujewa nakasa ko ma rasa rai baki ɗaya.

 

Kafin gana ,birnin kudu kg, Jigawa

 

Auwala Ado ya kai ɗan sa Haruna Auwala ofishin ƴan vigilant

 

Asp Lawan Shisu Adam, Kakakin ƴan sanda

 

Ya kai ɗan nasa ne zuwa ofishin ƴan bulala saboda ya saci masara a gona.

 

Bayan sun dake shi sun yi masa gwale-gwale, sai ya galabaita har a ka kai shi asibiti in da ya ce ga garinku nan.

 

Source: Daily Nigeria Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: