Ƴan-sanda sun cafke saurayin da ya ke yaudarar ƴan-mata ya gudu da wayar su ta salula

Rundunar Ƴan sanda ta Jihar Kano ta cafke wani saurayi mai suna Muhammad, wanda ya ƙware wajen yaudarar ƴan mata ya ce ya na son su, inda daga budurwa ta saba da shi, sai ya yaudare ta ya gudar mata da wayarta ta salula.

 

A wata sanarwa da Kakakin Rundunar Ƴan sandan, Abdullahi Kiyawa ya fitar a yau Laraba, dubun matashin ta cika ne bayan da wata budurwa da ke zaune a Sharaɗa ta kai ƙarar Muhammad Saifullahi ofishin ƴan sanda na yankinsu cewa ya yaudare ta ya gudar mata da wayarta.

 

Ta ce matashin ya zo gidansu ne ya kuma nuna ya na son ta ita kuma ta amince da shi, amma da ga bisani sai ya karɓe mata waya da ta ƙaninta ya ranta a na kare.

 

Budurwar ta yiwa ofishin ƙarin bayani da cewa lokacin da ya karɓe musu wayoyin, sai ya wayance cewa ya yar da mukullin babur ɗin sa, inda bayan sun taya shi nema, kuma suna tsaka da neman ne sai ya arce ya kuma kashe wayoyin.

 

Kiyawa ya ƙara da cewa jin haka, sai Kwamishinan Ƴan sanda, Sama’ila Shu’aibu ya umarci dakarun Kan-ka-ce-kwabo, wato Puff Ada, ƙarƙashin SP Abulrahim Adamu da su shiga farautar matashin.

 

Kwamishinan ya kuma umarci kakakin rundunar da ya kwarmata neman matashin a gidajen rediyo da talabijin.

 

Da ga nan ne ƴan sanda su ka shiga farautar sa har sai da su ka cafke shi a titin gidan zoo.

 

Matashin ya amsa laifin sa, inda kakakin ya ce ana ci gaba da bincike kuma za a gurfanar da shi a gaban ƙuliya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: