Ya Kamata a Tsige Shugaba Buhari, Cewar Sarki Sanusi II

Sarkin Kano na 14, kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Muhammad Sanusi II ya bayyana cewa, gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ta yi abinda za’a tsigeta.

 

Sanusi yace kuɗaɗen da ake kashewa wajen bayar da tallafin mai sun isa abinda zai sa a tsige shugaban ƙasar.

 

Ya bayyana cewa, an biya miliyoyin kuɗaɗe da sunan tallafi ba tare da bin doka ba.

 

Sarkin yace a yayin da Najeriya ke kashe kuɗi akan man fetur, kasashe irin su Ghana da Rwanda sun mayar da hankali wajen kashewa Ilimi da harkar kiwon lafiya kuɗi.

 

Sanusi yace kuma majalisar tarayya na gani amma bata abinda ya kamata, kamar yanda Vanguard ta ruwaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: