Dogo Gide ya kashe Damina a dajin Dansadau dake jihar Zamfara 

Rahotanni daga jihar Zamfara na bayyana cewar Damina wani hatsabibin dan ta’adda ya gamu da ajalinsa a wata kafsawa da suka yi da Dogo Gide a dajin Kunyambana dake Dansadau a yankin karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.

 

Damina daya ne daga cikin shugabannin ‘yan ta’addar daji da suke addabar mutane. Ko a a kwanakin baya an bayar da rahoton yadda ya bankawa wata mata wuta da ranta a dajin Zamfara. Damina an sha bayar da labarin satar mutane da garkuwa da su da yake yi, sannan kuka kwararren barawon shanu ne, ba shi fa imani domin an sha bada labarin yadda yake kone kauyukan mutane.

 

An dai kafsa wannan batarnaka ne tsakanin mayakan Dogo Gide da kuma na Damina a Cillin da Fammaje wasu yankuna guda biyu dake karkashin shi Damina a yankin Dansadau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: