An Cafke Mai Yi Wa Ƴan Luwaɗi Wayo Yana Damfararsu Kudi a Kaduna

An kama wani matashi mai yi wa ƴan luwaɗi wayo yana damfarar su kuɗi a Kaduna.

 

Matashin mai suna Abdulrahim Danagana, ya bude shafi ne a wani dandalin ƴan luwaɗi inda yake amfani da wannan damar yana nuna cewa ya yadda su yi da shi.

 

Yakan ce su aika masa da hotunansu tsirara, inda anan ne sai yayi amfani da waɗannan hotunan yace idan mutum bai bashi kuɗi ba, zai watsawa duniya ta gani.

 

Matashin ya riƙa amfani da sunayen ƙarya a shafin inda kuma ya yaudari ƴan luwaɗin kuɗin da suka kai Dala $8,420.

 

An dai gurfanar dashi a gaban kotu, inda aka ɗaga ƙarar zuwa 12 ga watan Satumba, sannan kuma an bayar da belinsa kan naira miliyan 1 da wanda zai tsaya masa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: