Kwalejin Tarayya A Jihar Bauchi Ta Kori Malamai Kan Zargin Lalata Da Dalibai

Hukumar kwalejin gwamnatin tarayya a Jihar Bauchi ta kori malamai biyu sakamakon kama su da laifin cin zarafi ta hanyar lalata da ɗalibai mata.

 

Shugaban kwalejin, Sanusi Gumau, shi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai yana mai cewa an ɗauki matakin ne yayin zaman majalisar zartarwar kwalejin na 98 da suka yi ranar Asabar.

 

Bayan samun ƙorafi daga ɗaliban, an kafa kwamatoci da zummar bincikar zarge-zargen waɗanda rahotonsu ne ya nuna cewa sun aikata laifin, a cewar Gumau.

 

“Dokokin kwalejin sun bayyana cewa idan aka samu zargi mai girma irin wannan matakin farko da ake ɗauka shi ne bincike,” a cewar shugaban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: