Rashin Girmama Addini Ne, Yanke-yanke Filayen Masallaci A Sayar Domin Yin Shaguna, Inji Sheikh Tijjani Bala

Rashin Girmama Addini Ne, Yanke-yanke Filayen Masallaci A Sayar Domin Yin Shaguna, Inji Sheikh Tijjani Bala

 

Fittacen Malamin Addinin Musulunci dake Kano Sheikh Tijjani Bala Kalarawi ya ajiye Mukaminsa na kwamittin Amintatun dake kula da masallacin Juma’a na Fagge dake jihar Kano.

 

Malamin ya ce ya ajiye mukaminsa ne ganin yadda ake ta gine-gine da yanka filaye babu gaira babu dalili a filayen Massallacin Juma’a dake Fagge.

 

Sheik Kalarawi ya bayyana hakan ne a cikin zantawar su da gidan Radio Express a wanan rana.

 

Malamin ya ce wannan tamkar rashin girmama wajan bautar Allah ne, tare da rashin kishin addinin musulunci.

 

Sheik Kalarawi ya ce ya sauke nauyin da Allah ya dora masa a matsayinsa na masani kuma Malami.

Leave a Reply

Your email address will not be published.