Kotu ta dakatar da shugaban jam’iyyar PDP na kasa

Kotu ta dakatar da shugaban jam’iyyar PDP na kasa

 

Wata babbar kotu a Jihar Ribas da ke kuduncin Najeriya ta dakatar da shugaban jam’iyyar PDP na kasar Uche Secondus. Shafin BBC Hausa ya ruwaito.

 

Wasu mambobin jam’iyyar biyu ne suka ruga gaban kotun don neman ta hana shugaban na PDP ayyana kansa, a matsayin shugaban jam’iyyar, ko ma jagorantar al’amuranta, bukatun da kotun ta amince da su.

 

Rikici dai na kara rincabewa a jam’iyyar PDP a baya bayan nan, inda ake ganin akwai gagarumin rashin fahimtar juna tsakanin gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike, da shugaban jam’iyyar PDPn na kasa Uche Secondus.

 

Ko da a makon jiya sai da dakataccen shugaban jam’iyyar ta PDP ya garzaya wajen tsohon shugaban Najeriya, Chief Olusegun Obasanjo, abun da ake alakantawa da bukatar ganin ya sa baki a takun sakar da ake ganin akwai tsakaninsa da gwamnan Jihar ta Rivers.

 

A `yan kwanakin nan ma sai da kwamitin amintattun jam`iyyar da sauran jiga-jiganta suka yi wani zama, inda suka takaita wa`adin shugaban jam`iyyar domin a yi babban taronta a watan Oktoba mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.