An nada Tunji Disu a matsayin wanda zai maye gurbin mukamin Abba Kyari

 

 

Shugaban rundunar Yan sanda na kasa Usman Alkali, ya amince da nada DCP Tunji Disu a matsayin shugaban rundunar jami’an fikira na IRT.

 

An dai nada DCP Tunji Disu ne don ya maye gurbin shugabancin rundunar ta IRT, da kuma cigaba da maida hankali wajan gudanar da aiki.

 

Yace hukumar za ta cigaba da gudanar da ayyukanta kamar yadda kasar ta tsara, da kuma bin dokokin kasashen ketare.

 

Kamin dai zabar DCP Tunji Disu a matsayin shugaban rundunar IRT, ya kasance shugaban rundunar (RRS) dake Lagos, karkashin hukumar Yan sandan Jahar Lagos.

 

Ya kuma yi aiki a matsayin jami’in leken asiri a Jahar Rivers, ya kuma jagoranci rundunar wanzar da zaman lafiya da aka aika a kasar Sudan.

 

DCP Tunji Disu, ya kammala karatun digirin sa a fannin Turanci, a Jami’ar dake Lagos, ya kuma cigaba da Masta nasa a Jami’ar dake Ondo.

 

Ya kuma samu damar halartar karatu a bangarori daban-daban a gida Nigeria dama kasashen ketare.

 

DCP Tunji Disu, zai cigaba da aiki nan take bayan kammala bincike nadinsa.

Wane fata zaku yi mishi?

Leave a Reply

Your email address will not be published.