An nada ‘Dan Shugaban Nigeria Yusuf Buhari a matsayin Talban Daura

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ziyaraci fadar Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Faruq Umar a yau Jumu’ah, inda anan take aka nada Yusuf Buhari a matsayin Talban Daura.
A yayin ziyarar tasa, Mai Martaba Sarkin Daura ya yi amfani da wannan damar, inda ya nada dansa Yusuf a matsayin Talban Daura.
Haka Zalika, tun bayan fitar da sanarwar bada sarautar Talban Daura a ranar sallah, wasu jaridu ciki har da Daily Trust, sun rawaito cewa a 2019 Sarkin Daura ya taba nada shugaban kasar Guinea Alpha Conde, wannan sarautar ta Talban Daura a yayin da ya gudanar da babbar sallar idi tare da shugaban kasa Buhari a garin Daura.
Haka Zalika, har yanzu masarautar Bata maida Martani akan wannan rahotanni da Jaridu suka ruwaita

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: