DA DUMU-DUMI: Tsohon gwamnan Jigawa a zamanin Soji Ibrahim Aliyu ya rasu

Tsohon gwamnan Jahar Jigawa a zamani mulkin Soji, Birgediya Janar Ibrahim Aliyu ya rasu a Kaduna a ranar Juma’a.

 

Gwamnatin Jahar Jigawa ta sanar da mutuwar Janar Ibrahim Aliyu a wani bayani da Habibu Nuhu Kila, mataimakin gwamnati na kafar sada zumunta.

 

Kamar yadda bayanin yake “Mai girma gwamnan Jahar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar, MON, mni, cikin bacin rai yana sanar da mutuwar tsohon gwamnan Jahar Jigawa a zamanin mulkin Soji Birgediya Janar Ibrahim Aliyu ya rasu a jiya Juma’a a Kaduna.”

 

“Gwamna Badaru Abubakar ya misalta mutuwar Birgediya Janar Ibrahim Aliyu a matsayin babban rashi ga mutanen jahar da ma gwamnatin Jigawa.”

 

” Yace Janar ya sadaukar da rayuwar sa wajan cigaban Jahar ta Jigawa.”

 

“Gwamna Badaru Abubakar ya yima marigayi Ibrahim Aliyu addu’a Allah ya jikanshi ya gafarta mashi, yana mika ta’aziyyar sa ga daukacin mutane Jigawa da kuma iyalansa kan wannan babbar rashin.”

 

Yayi mulkin jahar ne a tara ga watan Disamba na shekarar 1993 zuwa ashirin da biyu da watan Agusta na shekarar 1996 a lokacin Mulkin Janar Sani Abacha.

 

A farkon watan July ne na wannan shekarar, mataimakin shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar da wani titi a Jahar Jigawa inda yayi masa suna da Titin Janar Ibrahim Aliyu, bisa kokarin sa a zamanin mulkinsa.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: