Gwamnatin Tarayya ta amince da gina sabuwar Jami’ar koyar da Kere-Kere a Jigawa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da gina Jami’ar Tarayya ta Fasaha da Kere-kere a Babura ta Jahar Jigawa.

Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda da Ministan Ilmi Malam Adamu Adamu ya sanyawa hannu, aka turawa Gwamnatin Jahar.

Haka Zalika, Sanarwar ta bukaci Gwamnatin Jahar data samar da fili Mai tsawon Kadada 100, tare da samar da hanyoyi, da wutar lantarki, da kuma ya kasance kusa da ruwa.

Takardar ta kuma bayyana cewa, Jami’ai daga Ma’aikatar Ilmi, da Hukumar Kula da Jami’o’i da sauran masu ruwa da tsaki, zasu rika zuwa Jahar domin duba yanayin aikin, tare da tattaunawa da Wakilan Jahar, domin ganin an gudanar da aikin cikin sauri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *