Yanda aka kama wasu manyan yan bindiga bakwai (7) da shugabansu dauke da manya manyan makamai.
Acikin daren jiya 12/07/2021 ankama wata motar daukar yashi (tifa) dauke da makamai, bayan masu wannan motar sun loda makamai da alburusai sai sukabi da yashi sama suka rufe.
Yayin da motar ke yunkurin shiga daji akayi sa’a da motar jami’an sojoji tazo daura da wurin. Babban abinda yaja hankalin jami’an tsaro da su bincike wannan motar shine:
Direban wannan motar daukar yashin bayan da yaga motar jami’an tsaro tafe sai yake taka burki tare da kashe wutar motar yana mai jiran wucewar sojojin sannan ya dauke hanya zuwa shiga daji.
Kwatsam sai hankalin jami’an tsaro yabasu kamar wani abu na faruwa awurin. Jami’an tsaro sunyi gaggawar juyo motar su suka tunkare wurin da motar daukar yashin take, da isar su sai direban tifar yace motar ce ta lalace tun kamin a tambayeshi.
Sai jami’an sojoji suka fito daga motar su suka shiga motar daukar yashin domin ganin meke faruwa da motar. Da buga motar sai ta tashi, hakan yasa jami’an tsaro suka tsanan ta bincike akan wannan motar, bayan juye yashin dake cikin motar sai ga manyan makamai da alburusai da yawansu yakai 6000, bindigar AK-47 34, bindigar harbo jirgin sama uku, da rigar yan kunar bakin wake shida 6. da wasu manya manyan makamai.
Bayan an chafke direban sai yace aikoshi akayi kuma aka bashi kudi kimanin naira dubu dari biyu domin safarar wadannan kayan.
Jami’an tsaro suka tambayeshi suwaye suka aike ka din?? Yace yanzu zasuzo a bayan shi da karamar mota. Jami’an sojoji suka samu wuri suka buya suna jiran zowar wannan karamar motar. Cen bayan awa daya ( 1 hour) sai ga mutum biyar acikin wata karamar mota kirar (Jeep Toyota Highlander 2014) sai jami’an tsaro suka cafke su har diren babban motar tifa su shida (6).
Bayan ankama wadannan mutum shida din akaje dasu babban ofishin hukumar rundunar sojoji dake nan birnin kaduna domin gudanar da bincike. Direban babbar motar tifa yace zai fadi shugaban su idan har za’a sake shi yayi tafiyar sa, jami’an tsaro sukace eh sai yake bada labarin mazaunin shi wannan babban shugaban nasu dake daukar nauyin dukkan ta’addancin da sukeyi. Aka hada dashi aka kamo suka cika su bakwai (7).
Videon wannan lamarin yanada yawa zai iya kai wa (1 to 2 hours) Kubi wannan link din zuwa YouTube acen ne zamu dora video abunda yafaru domin ku kalla. Karku manta Kuyi Subscribe domin samun wasu video aduk lokacin da muka dora 👇
~ New Nigerian Chief Of Army Staff.