Malam Abduljabbar ya sake gindaya sharuɗan tuba

Sheikh Abduljabbar Kabara ya sake gindaya sharuɗa ga malaman Kano, matuƙar da gaske suna so ya tuba daga abin da suke zargin sa.

 

Malamin ya ce, har yanzu ba a gamsar da shi da hujjojin da suka fi nasa ba.

 

Ya ce, “Ya za a yi na yi karatu awa biyu zuwa uku ina warware matsala, sannan a yanko minti biyar a ce sai na ce kaza cikin minti goma.

 

“Me ya hana a ɗauko karatun gaba ɗaya a tattauna?”.

 

Ya ƙara da cewa, indai za ayi haka, to ba a biyo hanyar da ake cewa, ana so na tuba ba, ba da gaske ake ba, ba kuma gyara ake cewa ana so ba.

 

Malamin ya kuma ƙalubalancin malaman da su zo a biyo duk karatukan da yake yi, ba wai a gutsuro wata gaɓa ba.

 

Sheikh Abduljabbar ya ce, duk kalaman da ake jingina masa cewa yayi ɓatanci ba gaskiya bane, hassalima shi ƙoƙarin kare musulunci ya ke.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: