Masu Kasuwancin Giya Zuwa Kano Sun Koka Da Shugaban Hukumar KAROTA Dr Baffa Babba ‘Dan’agundi

Shugaban hukumomin KAROTA/CPC a jihar Kano Dr Baffa Babba ‘Danagundi ya zamowa masu safarar giya zuwa jihar Kano tashin hankali duba da muguwar asara da suke tafkawa ta hanyar kame motocinsu da hukumar KAROTA ke yi karkashin Dr Baffa Babba ‘Dan’agundi tare da mika su hukumar Hisba.
Masu kasuwancin sun koka da Dr Dan’agundi ne bisa hana su bacci da ido biyu da ya jima ya na yi, suna masu cewa yana janyo musu mummunar asara a kasuwancinsu.
Sun kuma yi korafin cewa hukumar hisba ce ke da alhakin kamun giya a jihar Kano ba hukumar KAROTA ba.
Sai dai Dr Dan’agundi ya jaddada cewa zai kara kaimi wajen dakile kasuwancin giya a jihar Kano kamar yadda addinin musulunci da dokar jihar Kano suka tanada, bugu da kari dokar kasa tuni ta bada dama ga kowanne dan kasa wajen dakile abin da ya gani ana yi ba daidai ba, haka addini ma ya yi umarni da hana mummuna.
Tun zuwansa hukumar KAROTA Dr ‘Dan’agundi, masu safarar magungunan bogi zuwa Kano da masu siyar da gurbatattun kayan masarufi a jihar Kano suka shiga halin ni ‘yasu bisa hana su rawar gaban hantsi da Dr Baffa Babba ya ke yi, kokari da jajircewarsa ce ta sa gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya nada shi a matsayin shugaban hukumar CPC, hukumar kula da hakkin siye da siyarwa ta jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published.