Dole Ne Gwamnati Tayi Sulhu da ‘Yan Ta’adda, Kuma Ta daina Tura Sojoji Suna Ruwan Bama-Bamai Ga Resu Matukar Ana Son a Daina Daukar Dalibbai~ inji Sheakh Gumi

Fitaccen malamin addinin musulunci a Najeriya Sheakh Ahmad Gumi ya bayyana cewar, ya zama dole ga gwamnatin kasar nan ta yi zaman sulhu da ‘yan bindiga don samun saukin kai hare-hare a makarantu.
Malamin ya bayyana cewar, “gwamnati na tura jami’an soji suna ruwan bama-bamai kan ‘yan bindiga, ya ce wannan ba zai janyo komai ba banda rikici”
Malamin dan asulin jihar kaduna dake Arewacin Najeriya yayi magana ne kan dauke dalibban kwalejin gwamnatin tarayya ta birnin Yauri a jihar kebbi da ‘yan bindiga suka yi.
Fitaccen malamin ya bayyana cewar, cijewar gwamnati na kin amuncewa da yin sulhu da ‘yan bindiga ba zai haifar da komai ba illa rura wutar rashin tsaro a kasar.
Ya baiwa gwamnatin tarayya shawarar cewar, ta lamunce da hawan teburin sulhu da ‘yan bindiga ba illa bane.
Ya kuma umurci gwamnati da ta umurci jami’an tsaro dasu daina jefawa ‘yan ta’adda bama-bamai, ya ce hakan zai iya janyo wata musifa ta daban daga ‘yan bindigar idan suka tunzura.
Me zaku Ce?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: