Buhari Ya Umurci Ministan Sadarwa Sheikh Pantami, Da Wasu Ministoci Da Su Tattauna Da Twitter

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, Ministan Shari’a, Abubakar Malami su tattauna da kamfanin Twitter game da haramta ayyukan kamfanin a Nijeriya.
Gwamnatin tarayyar Nigeria ta dakatar da Twitter ne kan zargin ana amfani da ita wurin raba kan yan kasa da karfafa masu neman tada rikici a kasar.
Duk da matsayin lamba daga kungiyoyin kare hakkin mutane da kasashen waje, gwamnatin Buhari ba ta janye dakatarwar ba.
Amma a cikin sanarwar da Lai Mohammed, Ministan Labarai ya fitar a ranar Talata, ya sanar cewa gwamnati ta shirya wata tawaga da za ta tattauna da Twitter.
Bayan Fashola, sauran ministocin da ke cikin tawagar sun hada da Isa Pantami, Ministan Sadarwar da tattalin arzikin zamani, Chris Ngige, Ministan Kwadago, da Geoffrey Onyeama, Ministan harkokin kasashen waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: