Dan Kwallon Nijeriya, Abdullahi Shehu Ya Auri ‘Yar Fim

A yau ne aka daura auren Fitaccen Dan wasan kwallon kafar Nijeriya, Abdullahi Shehu, da Amaryar sa wadda jarumar Finafinan Hausa ce mai suna Naja’atu Muhammad Suleman, wadda aka fi sani da “Murjanatu ‘Yar Baba”

 

An daura auren bayan an gama sallar Juma’a a garin Kano.

 

Jaruma Naja’atu, ta fara fitowa a Finafinan Kannywood tun tana ‘yar shekara 10 da haihuwa.

 

Kadan daga cikin Finafinan da fito sun hada da Murjanatu ‘Yar Baba da Auren Gaja da Hakkin Rai da kuma Harira” da sauransu.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.