Hauhawar farashin kayayyaki ya sanya ƴan Najeriya miliyan 7 cikin ƙangin talauci – Bankin Duniya

Kwanaki uku bayan jawabin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi da ke cewa, gwamnatin sa, ta fitar da al’ummar ƙasar nan sama da miliyan goma daga ƙangin talauci, bankin duniya ya fitar da wani rahoto da ke cewa, hauhawar farashin kayayyaki ya sanya mutane miliyan bakwai cikin ƙangin talauci.

 

Wannan rahoto na bankin duniya na zuwa ne a lokaci guda da hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ke cewa, an samu saukowar farashin kayayyaki da akalla kasa da kaso ɗaya a watan jiya na Mayu.

 

A cikin wata sanarwa da bankin na duniya ta fitar a jiya talata, ta ce, hauhawar farashin kayayyakin abinci wanda shine kaso sittin cikin dari na ƙididdigar hauhawar farashin da aka samu a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.